• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MATASAN KIRISTA: ZA MU HADA KAI DA KUNGIYAR MATASA MUSULMI

ByNoblen

Nov 7, 2020

Reshen matasa na kungiyar kiristoci ta Najeriya YOWICAN ya ce zai hada kai da kungiyar matasa musulmi NACOMYO don gano bakin zaren hana sake gudanar da zanga-zangar da za ta lalata dukiyar jama’a koma kai wa ga asarar rayuka.

A taron manema labaru a helkkwatar “CAN” a Abuja, shugaban reshen matasan Apostle Nyeneime Andy ya ce kungiyar na mara baya ga matasa ko masu zanga-zanga na hakika ba masu lalata dukiyar jama’a ba.

Apostle Andy ya ce kungiyar ta yi Allah wadai da batun kisan da a ka ce an yi a Lekki a Lagos lokacin zanga-zangar endsars; duk da daga bisani ya ce ba zai yi karin bayani ga batun ba don a na gudanar da bincike.

Daga bisani sakataren kungiyar Abel Agwuche ya ce sun tabbatar da an kashe dan kungiyar su daya ne a Lekki don haka ba lalle ne a dau batun a matsayin kisan kare dangi ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “MATASAN KIRISTA: ZA MU HADA KAI DA KUNGIYAR MATASA MUSULMI”
 1. I loved as much as you’ll receive carried out right here. The sketch is attractive,
  your authored material stylish. nonetheless,
  you command get bought an shakiness over that you wish be delivering the
  following. unwell unquestionably come more formerly again as exactly
  the same nearly very often inside case you shield this increase.

 2. Heya i am for the first time here. I came across this board and I find It really useful
  & it helped me out much. I hope to give something back and
  aid others like you aided me.

 3. I pay a visit each day a few web sites and websites to read articles,
  except this webpage presents quality based writing.

Leave a Reply

Your email address will not be published.