• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MATAR CHUBA OKADIGBO TA ZAMA MEMBA A HUKUMAR KAMFANIN FETUR

ByHassan Goma

Sep 20, 2021 ,

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada matar tsohon mataimakin sa a takarar shugaban kasa Sanata Chuba Okadigbo wato Margaret a matsayin memba a hukumar kula da kamfanin fetur na Najeriya NNPC.

Shugababan a matsayin sa na babban ministan fetur ya ba da umurnin fara aikin hukumar karkashin Ifeanyi Ararume.

Sauran membobin sun hada da Tajuddeen Umar daga arewa maso gabar, Mohammed Lawal daga arewa maso yamma, Barista Constance Harry Marshal daga kudu maso kudu sai Pious Akinyelure daga kudu maso yamma.

Da alamu ayalan mukarraban shugaban a siyasar narkakkiyar jam’iyyar ANPP sun samu mukami a hukumar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *