• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MATAKIN DA A KA DAUKA KAN NURU KHALID YA YI TSAURI-DAYA DAGA LIMAMAN ANGUWAR APO

Rahotanni na nuna wasu mazauna anguwar APO a Abuja wato anguwar ‘yan majalisar dokokin Najeriya na niyyar kwabe shugaban kwamitin masallatan anguwar Sanata Sa’idu Dansadau biyo bayan dakatar da limamin babban masallacin jumma’a na anguwar Sheikh Nuru Khalid.

Dakatarwar da ta biyo bayan hudubar sallar jumma’ar makwan jiya, ta haddasa suka mai tsanani musamman a kafafen sadarwar yanar gizo.

Nuru Khalid wanda ya bukaci jama’a kar su fito zabe matukar ba a inganta tsaro gabanin zaben ba, ya gamu da matakin kwamitin masallatan inda hatta tafsirin da ya saba na ramadan, a ka nada wani limami ya maye gurbin sa.

Khalid da kan shirya shan ruwa da mabiya addinin kirista a masallacin don karfafa fahimtar juna na tsakanin addinai, na daukar salon wa’azin kowa ya zo a tafi tare, ko ma a daina mayar da hankali kan batun bidi’a a rika karfafa batun tabarbarewar tsaro.

Limamin masallacin ZONE BA na anguwar ‘yan majalisar Ibrahim Auwal Usama ya so shiga tsakani kan barazanar tsige Dansadau daga kujerar don samun dawo da Sheikh Khalid da a ke yi wa taken “DIGITAL IMAM” don yanda yak an yi amfani da na’ura mai kwakwalwa kan mukamin sa.

In za a tuna a sallar idin azumin bara, an samu irin wannan takaddama tsakanin Imam Usama da Dansadau, yayin da Dansadau din ya yi wuf ya karfe na’urar magana ya musanta sukar gwamnatin Buhari da a ke yi cewa ba ta tabuka abun kirki ba.

Imam Usama ya sa an yi zaben marawa ra’ayin sa baya ta hanyar kabbara har sau uku inda jama’a su ka goyi bayan cewa gwamnatin ta gaza.

Anguwar dai da a tarihi ta ‘yan majalisa ce amma yanzu ta zama kusan gidajen tsoffi da wasu ‘yan majalisa masu ci tun sayar da gidajen da gwamnatin Obasanjo ta yi a dambarwar tazarce gabanin zaben 2007.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
9 thoughts on “MATAKIN DA A KA DAUKA KAN NURU KHALID YA YI TSAURI-DAYA DAGA LIMAMAN ANGUWAR APO”
  1. Very interesting information!Perfect just what I was looking for! “Oh, I don’t blame Congress. If I had 600 billion at my disposal, I’d be irresponsible, too.” by Lichty and Wagner.

  2. Howdy! Do you know if they make any plugins to help with Search Engine Optimization? I’m trying to get my blog to rank for some targeted keywords but I’m not seeing very good gains. If you know of any please share. Appreciate it!

  3. It’s a pity you don’t have a donate button! I’d most certainly donate to this brilliant blog! I suppose for now i’ll settle for bookmarking and adding your RSS feed to my Google account. I look forward to brand new updates and will share this site with my Facebook group. Chat soon!

Leave a Reply

Your email address will not be published.