• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MATA NA NEMAN KASHI 30% ZUWA 40% A GWAMNATIN BAZOUM

ByYusuf Yau

Apr 10, 2021

Kungiyoyin mata a jsmhuriyar Nijar sun nuna rashin gamsuwa ga yawan mukaman da sabon shugaban jamhuriyar Nijar Bazoum Muhammed ya nada.

Matan dai na bukatar akalla samu kashi 30% zuwa 40% a majalisar zartarwar kasar.

Cikin wajen ministoci 40, shugaba Bazoum Muhammed ya nada mata biyar ne.

Matan sun ce in an duba rawar da su ka taka a yakin neman zabe, mukamai biyar sun yi mu su kadan.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da a ke sharhin jam’iyyun adawa da su ka hada kai da PNDS taraiya ta lashe zabe ba su samu wakilcin da ya dace ba a gwamnatin.

Shugaba Bazoum ya zabo Oummadou Muhammadou a matsayin firaministan inda ya gaji ofishin tsohon firaminista da ya shafe shekaru 10 kan kujera Briji Rafini.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *