• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASU ZANGA-ZANGAR RASHIN TSARO A AREWA SUN CIGABA DA FITOWA A ABUJA

ByNoblen

Dec 15, 2021 , ,

Masu zanga-zangar neman karfafa tsaro a yankin arewacin Najeriya sun cigaba da fitowa a Abuja rike da kwalaye na rubuce-riubucen bukatun su.
Duk da dai mutanen ba su da yawa a ido, amma sun ci nasarar yayata muradun su a kafafen yanar gizo da wasu gidajen rediyo da talabijin.
Gwamnati dai ba ta tsangwamar masu zanga-zangar kai tsaye in ka debe hana su ficewa daga yankin dandalin UNITY da ke daura da hotel din nan na Hilton.
An samu labaru na gaiyatar wasu daga masu zanga-zamgar a waje da Abuja daga jami’an tsaro don tambayoyi.
Fadar Aso Rock ta bakin Garba Shehu ta ce ba ta takaddama da masu zanga-zangar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MASU ZANGA-ZANGAR RASHIN TSARO A AREWA SUN CIGABA DA FITOWA A ABUJA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *