• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASU ZANGA-ZANGAR KAUDA SARS BA SU JANYE BA DUK DA SOKE RUNDUNAR

ByNoblen

Oct 14, 2020 , , ,

Masu zanga-zangar neman kauda rundunar ‘yan sandan yaki da ‘yan fashi “SARS” sun cigaba da gudanar da zanga-zangar a Abuja duk da sanar da soke rundunar da babban sufeton ‘yan sanda Muhammad Adamu ya yi.
Da alamu masu zanga-zangar na neman a hukunta jami’an ne na tsohuwar rundunar da su ka ci zarafin jama’a da aikata kisan kai.

Wasu kuma na da ra’ayin cewa wata dabara kawai rundunar ‘yan sandan ta yi ta hanyar sauya sunan SARS zuwa SWAT.
Za a jira a ga yanda wannan lamarin zai kawo karshe da ya ke neman juyewa zuwa tsamar mutan arewa da kudu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.