• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASU ZABE A NAJERIYA DA DAMA NA MARABA DA AIKIN GYARAN DOKAR ZABEN FIDDA GWANI ZUWA ‘YAR TINKE WATO KATO-BAYAN-KATO

ByYusuf Yau

Oct 17, 2021

Masu zabe da dama a Najeriya na maraba da aikin gyara dokar zabe da za ta ba da damar gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyu ya koma ta hanyar ‘yar tinke wato kato-bayan-kato.
Duk da dai gyaran sai ya samu amincewar karshe daga kwamitin bai daya na majalisun dokokin Najeriya biyu; tuni mutane ke maraba da hakan da kwarin guiwar da shi za a gudanar da zaben 2023.
Zuwa yanzu ba a fara samun martani daga masu rike da kujerun zartarwa irin gwamna zuwa shugaban kasa ba, amma masu kada kuri’a da akasarin ‘yan jam’iyya da zaben wakilai ba ya kyautatawa muradun su, sun ce fidda gwani ta ‘yar tinke “OPTION A4” zai yi maganin dauki-dora ko saye wakilai.
Ga Abdullahi Garba Gombe na jam’iyyar adawa ta AD, salon zaben na keke-da-keke zai yaye labulen da ‘yan siyasar jari hujja ke fakewa a ciki, inda ba sa fitowa sai lokacin zabe.
Shi ma tsohon kansila a mazabar Kalmai daga Billiri a arewa maso gabar Nathan Kalfaddo ya ce ya na maraba da tsarin da fatar jam’iyyar sa ta PDP za ta karfafa kudurin don amincewa da shi.
Wadannan ra’ayoyin sun sha bamban da na tsohon darakta a hukumar zaben Najeriya INEC Kabiru Dahiru da ke cewa rudani zaben zai kawo a sabon zamani kuma mafita it ace damka zaben fidda gwani ga hukumar zabe.
Magudin zabe dai ya kan fara ne daga cikin jam’iyyu kafin na neman kujerar siyasa inda har yanzu a Najeriya a ke cewa gyara yau da jiya ko gara jiya da yau.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
5 thoughts on “MASU ZABE A NAJERIYA DA DAMA NA MARABA DA AIKIN GYARAN DOKAR ZABEN FIDDA GWANI ZUWA ‘YAR TINKE WATO KATO-BAYAN-KATO”
 1. The other day, while I was at work, my sister stole my iPad
  and tested to see if it can survive a 40 foot drop,
  just so she can be a youtube sensation. My iPad is
  now destroyed and she has 83 views. I know this is completely off topic but I
  had to share it with someone!

 2. Hi there this is kind of of off topic but I was wondering if
  blogs use WYSIWYG editors or if you have to manually code with
  HTML. I’m starting a blog soon but have no coding experience so I wanted to get guidance from someone with experience.
  Any help would be greatly appreciated!

 3. Pretty component to content. I simply stumbled
  upon your website and in accession capital to claim that I acquire actually
  loved account your blog posts. Any way I’ll be subscribing in your
  feeds and even I fulfillment you get right of entry to constantly rapidly.

 4. Hello! I just wanted to ask if you ever have any issues with hackers?
  My last blog (wordpress) was hacked and I ended up losing several weeks of hard work due to no back up.
  Do you have any solutions to prevent hackers?

Leave a Reply

Your email address will not be published.