• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASU YAWAN SHEKARU SU KAUCE SU BA MU DAMAR MULKIN NAJERIYA A 2023-MATASA A ZAUREN VOA

ByNoblen

Jan 4, 2022

Alamun da ke nuna sashin matasa a Najeriya sun kosa da jiran cikakkiyar damar jagoranci, sun bukaci tsofi su kauce su ba su fage don hawa madafun iko a 2023.
Matasan na magana ne a wajen daukar sabon shirin zauren matasa na VOA na farko a bana da a ka gabatar a ofishin muryar Amurka na Abuja.
Ahmadu Adamu Giade da ke kan gaba a wannan ra’ayin, ya ce ba alamun wadanda su ka dade kan madafun iko na da ranar da za su buda ‘yar dama ga matasa su hau karaga.
Shi ma matashi daga Yobe Yau Yakubu ya lissafa wasu daga shugabanni ne a Najeriya da su ka samu damar gudanar da mulki kuma su ka yi abun azo a gani a yayin da su ke da karancin shekaru.
Dattijuwa a taron Hajiya Mama Balaraba ta marawa matasan baya ta na mai cewa akwai bukatar garambawul ga masu jagoranci da ke son makalewa kan mulki har iya rayuwar su.
Karshe dai matasan sun nanata mara baya ga dokar nan ta zaben ‘yar tinke a fitar da gwani na jam’iyyu da shugaba Buhari ya ki sanyawa hannu, inda majalisa ta ce za ta duba lamarin a sabuwar shekarar nan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “MASU YAWAN SHEKARU SU KAUCE SU BA MU DAMAR MULKIN NAJERIYA A 2023-MATASA A ZAUREN VOA”
  1. Hey I know this is off topic but I was wondering if you knew of any widgets I could add to my blog that automatically
    tweet my newest twitter updates. I’ve been looking for a plug-in like this for quite some time and was hoping maybe you would have some experience with
    something like this. Please let me know if you run into anything.
    I truly enjoy reading your blog and I look forward to your new
    updates.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *