• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASU SHEKARU 18-35 NE ZA MU BARI SU ZAMA SHUGABANNIN MATASA A MAZABU-APC

Jam’iyyar APC mai mulki a taraiya ta kafa ka’idar sai masu shekaru daga 18-35 ne za su zama shugabannin matasa a matakin mazabu da kananan hukumomi.

Matakin ya zo gabanin zaben da za a gudanar a karshen watan nan na yuli.

Shugaban matasa na kwamitin rikon jam’iyyar Barista Ismaeel Ahmed ya kawo tsarin da ya samu karbuwa a kwamitin rikwan.

Ismaeel ya ce wannan ya shafi dabarun zaben 2023 inda ya ce masu hangen nesa sun gano matasa ne za su kai kowace jam’iyya ga gaci.

Shi ma shugaban kwamitin rikwan jam’iyyar Mai Mala Buni ya ce jam’iyyar za ta fadada tsarin kowa ya samu damar taka rawa don an daukewa sabbi da wadanda su ka dawo jam’iyyar duk shingen da zai hana su takara.

APC ta ce lokacin zaben matasa na jihohi da na taraiya za ta kara damar yawan shekarun zuwa 40.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP na cewa za ta iya karbar ragama a zaben mai zuwa duk da akwai wasu manyan ‘yan siyasa da ke shirin dibar jama’a daga manyan jam’iyyun don kafa wata sabuwar gagarumar jam’iyya da ta saba da APC da PDP.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *