• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASU SAYEN KAYA SU BOYE SAI SUN YI TSADA BA SU KYAUTA BA-SHEIKH ZAKARIYAH AJIYA

ByNasiru Adamu El-hikaya

Nov 29, 2021

Shehun malamin Islama Zakariyah Ajiya ya nuna takaici yanda wasu ‘yan kasuwa ke saye kayan abinci su na boyewa.
A hudubar sa a masallacin jumma’a na Bolari, Gombe, Sheikh Zakariyah Ajiya ya ce da alamu jin shirin kara farashin man fetur a badi ya sa wasu dukufa wajen sayan kayan abinci har ma wanda ya ke gona, su na kai wa ma’ajiya su na boyewa don in ya yi dan karen tsada su fitar su sayar don cin kazamar riba.
Sheikh Ajiya ya nuna ba amfanin tara dukiya ta kowane irin hali don da zarar mutum ya bar duniya sai abun kirkin da ya shuka ne zai amfane shi.
Malamin ya gargadi mutane su shuka alheri don cin gajiyar hakan a lahira don ka da bayan sun rasu wasu su yi ta gwagwarmayar watanda da dukiyar su ba tare da ma tuna yi mu su addu’a ba.
A nan malamin ya ba da labarin wata mata da mijin ta ya rasu sai ta sanya kananan kaya ta shiga daki ta yi ta tikar rawa ta na murna don jibgin dukiyar da za ta ci gado.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
5 thoughts on “MASU SAYEN KAYA SU BOYE SAI SUN YI TSADA BA SU KYAUTA BA-SHEIKH ZAKARIYAH AJIYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.