• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASU SATAR MUTANE SUN ADDABI AL’UMMAR NEJA INDA HAR SU KA SHIGO BABBAN BIRNIN JIHAR

Masu satar mutane sun haifar da tsoro ga al’ummar jihar Neja inda su kan sace da neman kudin fansa wani lokacin har da kisa.

Lamarin ya kara muni bayan shigowar barayin har cikin babban birnin jihar Minna su ka bude wuta kan jami’an sintiri a anguwar Maitumbi.

Harin birnin Minna ya yi sanadiyyar raunata mutum biyu da sace wasu mutum biyu.

Majiyar jaridar Daily Trust ta baiyana cewa barayin sun yi amfani da wayar daya daga wadanda su ka sacen su ka nemi kudin fansa Naira miliyan biyar.

Mazauna gefen Maitumbi sun shiga firgicin yiwuwar sake kawo hari don haka su ka nemi mafaka a wata makarantar firamare.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MASU SATAR MUTANE SUN ADDABI AL’UMMAR NEJA INDA HAR SU KA SHIGO BABBAN BIRNIN JIHAR”
  1. Admiring the commitment you put into your site and in depth information you provide.
    It’s great to come across a blog every once in a while that isn’t the same outdated rehashed information. Wonderful read!
    I’ve bookmarked your site and I’m adding your RSS
    feeds to my Google account.

Leave a Reply

Your email address will not be published.