• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASU SATAR MITANE SU TUBA DON SU NA BATA SUNAN AREWA-FAROUK ADAMU ALIYU

A cigaba da neman bakin zaren warware kalubalen masu satar mutane dattawa, manyan ‘yan siyasa, malaman addini da sarakunan gargajiya na kira ga duk wanda bai zama mai kunnen kashi a barayin ba, ya jingine makami ya dawo na kirki.

Biyo bayan kokawar da Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Bamalli ya yi na yanda barayin su ka addabi masarautar sa, mukarrabin shugaba Buhari Alhaji Farouk Adamu Aliyu ya ce kasancewar barayin na ikirarin su ‘yan arewa ne, su daina tozarta arewa.

Farouk Aliyu ya ce lamarin na da ban mamaki inda a kan samu matasa makiyaya da ke fakewa da an sace mu su shanu, su kan auka wannan muguwar dabi’ar da a karshe za ta yi sanadiyyar rayuwar su ko ta dangin su.

Aliyu wanda ya ce shi ma Bafulatani ne gaba da baya, ya ja hankalin makiyayan cewa an fahimci korafin su a yanzu kuma ba ribar sacewa da kara talauta yankin su.

A na  sa sharhin dattijon siyasar arewa Ajiyan Akko Alhaji Lamido Umar Chikaire ya ce halin da a ka shiga ya zo ne bayan sakaci da halin ko in kula ga mazauna daji tsawon shekaru.

A taron Miyetti Allah kwanan nan, shugabar mata ta kungiyar ta Ekiti Amina Ibrahim ta ce a kan samu kowace kabila a barayin kuma sai an daina furta kalamai masu zafi kafin samun maslaha.

Yayin da jami’an tsaro ke cewa su na fafatawa don murkushe miyagun irin, talakawa na cewa sai sun daina jin a na sace yara daga makarantu kafin su yi ajiyar zuciya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
56 thoughts on “MASU SATAR MITANE SU TUBA DON SU NA BATA SUNAN AREWA-FAROUK ADAMU ALIYU”

Leave a Reply

Your email address will not be published.