• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASU RIKE DA KAMBEN PREMIER NA KASAR INGILA SUNYI KUNNEN DOKI

A cigaba da wasan premier na kasar ingila a sati na goma Brighton sun karbi bakuncin Liverpool masu rike da Kofin premier league inda suka tashi ci daya da daya (1-1) a minti na 34 Muhammed Salah ya zura masu kwallon amma alkalin wasa ya kasheta, sai a minti na sitting sabon Dan kwallon Liverpool diogo jota ya zura kwallo, yayin da a minti na casa’in Brighton suka samu bugun daga Kai sai mai tsaron gida inda Pascal gross ya zura kwallon Aka tashi kunnen Doki.

Bayan an tashi wasan Liverpool suna saman teburin premier league da maki 21 kafin Tottenham su buga wasansu a gobe, samun nasarar Tottenham, Chelsea da leicester zai sauko da Liverpool zuwa mataki na hudu domin dukkansu sunada maki Sha takwas ne kuma sunfi Liverpool zura kwallaye, yayinda Brighton suke a mataki na goma Sha shidda da maki goma.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “MASU RIKE DA KAMBEN PREMIER NA KASAR INGILA SUNYI KUNNEN DOKI”
  1. I read this paragraph completely about the comparison of most up-to-date and earlier technologies, it’s awesome article.

Leave a Reply

Your email address will not be published.