• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASU KIRAYE-KIRAYEN A SAUKENI YARA NE- SHUGABAN PDP AYU  

Shugaban jam’iyar PDP Iyorchia Ayu yace masu kira a sauke shi daga mukaminsa yara ne.
 
Idan ba’a manta ba gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike  ya ya bukaci sauke Ayu daga mukamin a matsayin sharadin samun dai-daito tsakanin sa da Atiku Abubakar don samun mara bayansa a babban zaben 2023 mai zuwa.
 
Wutar rikici tsakanin yan jam’iyar biyu ta samo asali tun bayan lashe zaben fidda gwani da Atiku Abubakar yayi da kin daukar Wike a matsayin mataimakin shugaban kasa a babban zabe mai zuwa 2023.
 
Ayu yace an zabe shi shugaban ne bisa tsarin  dokokin jam’iyar ta PDP da ya bashi dama yayi shekara 4, don haka nasarar Atiku bata shafi kujerarsa ba.
 
“Ba zamu bar mutum daya ya bata mana jam’iya ba”, cewar Ayu.
 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.