• Fri. Jan 28th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASU HALI SU TABBATAR SUN FIDDA ZAKATUL FITR-SHEIKH BALA LAU

ByYusuf Yau

May 12, 2021

Shugaban JIBWIS Imam Abdullahi Bala Lau ya bukaci duk mai sukuni ya tabbatar da fitar da Zakatul fitr don tallafawa dimbin masu bukata.

Shehun malamin ya ce wannan zakkah ta na da tasirin gaske ga gidaje da dama da kan kwana ba tare da tabbacin samun abun sawa a girki ba.

Malamin ya bukaci gaggauta fitar da zakkar don marar sa galihu da ma marayu su samu abinci kamar sauran jama’a a ranar sallah.

Baya ga ma zakkar, malamin ya ba da shawarar ihsani na kudin cefane ga wanda ke da hali don ya zama gidajen makwabta duk su samu miya mai armashi.

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce mai yin sadaka don neman yardar Allah na daga cikin mutum 7 da za su shiga inuwar al’arshi ranar kiyama.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *