• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASOYA MARIGAYI SHUGABA UMARU ‘YAR’ADUA NA JUYAYIN CIKA SHEKARU 11 DA RASUWAR SA A LARABAR NAN

A larabar nan 5 ga watan Mayu, tsohon shugaban Najeriya Umaru Musa ‘Yar’adua ke cika shekaru 11 da rasuwa bayan fama da jinyar da ta kai shi asibiti Saudiyya inda bayan dawowa rai ya yi halin sa a fadar Aso Rock.

In za a tuna bayan rasuwar marigayin, mataimakin sa Goodluck Jonathan ya zama shugaba ya kammala wa’adin zuwa 2011 ya sake tsayawa zabe ya cigaba da mulki har 2015 inda shugaba Buhari ya yi nasara a kan sa.

A zantawar sa da manema, minista a zamanin marigayin Ikra Aliyu Bilbis ya ce marigayin na daga nagartattun shugabanni da Najeriya ta taba samu da ya kirkiro shirye-shirye ciki har da dakatar da hare-haren tsageran Neja Delta, umurnin murkushe Boko Haram, jawo ruwan teku zuwa arewa da sauran su.

Tun bayan mutuwar marigayin, ba a faye jin wani labari da ya shafe shi ko iyalin sa ba a kafafen labaru in ka debe tunowa da juyayin mutuwar sa a karagar mulki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *