• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASAR ZA TA DAU DUK MATAKIN DA YA DACE DON KARE KOGIN NILU

ByNoblen

Jul 10, 2021 ,

Ministan wajen Masar Sameh Shoukry ya ce kasar sa za ta dau duk matakan da su ka dace wajen kare hakkin ‘yan kasar daga barazana da Habasha ke yi wa kogin Nilu.

In ba a manta ba Habasha na gina katafaren dam don tara ruwan aikin samar da wutar lantarki da hakan ke neman kange ruwan da ke malala zuwa Masar da Sudan.

Dhoukry ya ce Masar za ta cigaba da bin tsarin tattaunawa ta majalisar dinkin duniya kan aikin dam din na Habasha don samun sulhu, amma kuma za ta dau matakan kare jama’ar ta daga barazanar asarar kogon Nilu mai dogon tarihi da har wake-wake a ka yi ma sa don aikin noman rani da raya kasa.

Masar da Sudan sun gabatar da korafin su ga kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya don sa baki da hana Habasha cigaba da fadada matattarar ruwan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *