• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASAR TA BUKACI FICEWAR DAKARUN KETARE DAGA KASAR LIBYA

ByNoblen

Jun 21, 2021 , ,

Kasar Masar ta bukaci sojojin kasashen ketare da ke Libya su fice daga kasar yayin da gwamnatin rikwam kwarya ke shirya lamuran zabe zuwa 24 ga watan disambar bana.

Ministan wajen Masar Sameh Shoukry ya baiyana bukatar a ganawa da manema labaru na hadin guiwa da takwarar sa ta Libya Najla Mangoush.

Shoukry ya ce Masar na mara baya ga gwamnatin rikwan kawaryar don samun zaman lafiya da tsaro a kasar ta Libya da ta shiga rudani tun kisan gilla ga shugaba Moammar Ghaddafi a 2011.

Hakanan zantawar ta shafi wani shirin babban taron salamar Libya a birnin Berlin na kasar Jamus.

Mangoush na ganin bayan taron Berlin za a samu nasarar hada kan sassan da ke rike da madafun iko a kasar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
34 thoughts on “MASAR TA BUKACI FICEWAR DAKARUN KETARE DAGA KASAR LIBYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.