• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASANA KIMIYYAR KIMIYYA NA NUNA DAMUWA KAN TSARIN BABBAN TARON APC DA BA BAYANAI

Masana kimiyyar siyasa na nuna akwai damuwa a tsarin shirin babban taron jam’iyyar gwamnati ta APC da ba cikakkun bayanai, kimanin kwana 5 gabanin taron.
Wannan ya kara daukar hankali bayan ganin an manna hotunan shugaban kwamitin sulhun jam’iyyar Abdullahi Adamu a cikin masu neman shugabancin jam’iyyar.
Rashin ganin ware yankunan da ‘yan takarar mukamai za su fito da ya bude kofar masu son takara daga dukkan yankunan arewa na fitowa, abun dubawa ne
Masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja Dr.Abubakar Umar Kari ya ce akwai fargabar komai zai iya faruwa game da zaben da ke dauke da ayar tambaya, shin an shirya gudanar da babban taron ko kuwa a’a.
Shi kuma memba a kwamitin rikwan jam’iyyar Sanata Yusu A Yusuf ya kaucewa ba da bayanai filla-filla kan babban taron da nun aba shi ne kakaki ko sakataren kwamitin ba, duk da ya na nuna shirin taron na nan a 26 ga watan nan.
Da ya ke sharhi kan babban taron, gwamnan Filato Simon Lalong ya baiyana abun da kan zama fargaba ga jam’iyyu kan manyan tarukan su, da yiwuwar rasa wadanda sakamako bai yi wa dadi ba.
Za a cigaba da zuba ido kan APC don faiyace tsarin taron ko daukar wani mataki na daban bisa ga abubuwan da ke gudana a halin yanzu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.