• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MASALAHA SHINE MATSAYINMU A SIYASA– KAWU SUMAILA.

Tsohon Wakilin Takai da Sumaila a majalisar tarayya 2003-2015, Kuma tsohon Mai bawa shugaban kasa shawara a majalisar kasa, Honourable Sulaiman Abdurrahman (Kawu Sumaila) yace samun masalaha a siyasa shine matsayin sa a kowanne mataki, “Alokacin da kasa ke cikin neman zaman Lafiya da ingantacciyar tsaro, musamman a yankunanmu na arewacin Najeriya, an wuce yanayin rikici akan shugabanci a ko wanne mataki.

Sammaila Wanda daya ne daga cikin manyan fitilun dake haska jam’iyyar gwamnati me ci ta APC, Kuma me neman kujerar majalisar dattawa ta kudancin Kano a tarayyaar Najeriya, yace wajibi ne a nemi hadin Kan al’umma da mu’amala Mai kyau domin samun cikakken zaman Lafiya da ci gaba Mai dorewa a Kano da kasa baki daya. Wadannan kalamai dai sun fito daga bakin shine a yayin wata tattaunawa da yayi da wakilai Sha tara na kananan hukumomin kudancin Kano daya gudana a ranar lahadi 5 gatan nuwamba a dakin taro na Centra hotel dake birnin Kano.

A karshe ya hori wakilan da su kasance ababen koyi wajen kiyaye daukan doka a hannu, da Kuma tabbatar da zaman Lafiya acikin al’umma

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.