• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MARAYU SUN YI MURMUSHI A ABUJA YAYIN DA SHEIKH BALA LAU YA RABA MU SU TALLAFI

Marayu sun yi dafifi a helkwatar JIBWIS a Abuja inda shugaban kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau ya raba mu su tallafin abinci, sutura har da kudin dinky.
Cikin murmushi, marayun daya bayan daya daga kananan hukumomin Abuja 6 su ka rika karbar tallafin don shirin karamar sallah kamar sauran yara masu iayaye da ke raye.
Sheikh Bala Lau ya kara da cewa daga bana za a fara gwada daukar nauyin yara marayu 20 a Abuja don su yi karatu su kammala a karkashin kungiyar, hakanan za a yi wani shirin aurar da mata da zawarawa da ba su da sukunin samun mai tallafa mu su.
“Irin wadannan yara marayu da ba su da iyaye, to su sani kungiyar Izala it ace iyayen su” inji sheikh Bala Lau, wanda ya ce da yardarm Allah za a fadada daukar nauyin zuwa sauran jihohi.
Shugaban kwamitin marayun na Abuja Alhaji Abdullahi Almaliki Diggi ya ce sun dau aikin a matsayin amana da kuma za su cigaba da gudanar da shi har iya rayuwar su.
An samu nasarar tara Naira miliyan 32 a matsayin gudunmawa ga marayun albarkacin tafsirin da Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ke gabatarwa a sabon masallacin helkwatar JIBWIS a Utako Abuja.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “MARAYU SUN YI MURMUSHI A ABUJA YAYIN DA SHEIKH BALA LAU YA RABA MU SU TALLAFI”
  1. I wanted to put you that tiny observation just to thank you very much the moment again on the superb methods you have provided on this website. This has been surprisingly generous of you to convey extensively what most people might have offered for an ebook to generate some profit for themselves, primarily considering that you might have tried it if you ever considered necessary. Those secrets additionally worked to become easy way to be aware that most people have the same desire similar to my very own to realize a good deal more around this issue. I’m certain there are lots of more fun occasions ahead for people who start reading your website.

Leave a Reply

Your email address will not be published.