• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MANYAN ‘YAN SIYASA NA KARA NUNA RASHIN MASLAHAR MULKIN KARBA-KARBA A NAJERIYA

Manyan ‘yan siyasar Najeriya musamman na yankin arewa na nuna rashin maslahar gudanar da dimokradiyya ta hanyar karba-karba.
Wannan tsari na karba-karba dai ba tanadin tsarin mulki ba ne amma ya zama wata hanya da jam’iyya mai mulki daga zamanin PDP ke bi don samun amincewa juna tsakanin yankin kudu da arewa.
Bayan gaza nasarar tazarce ta tsohon shugaba Obasanjo a 2007, PDP ta kawo tikitin ta arewa inda marigayi Umaru ‘Yar’adua ya hau mulki amma rasuwar sa a 2009 ta sa birkicewar tsarin.
‘Yan siyasar na cewa cigaba da karba-karba zai kara raba kan ‘yan Najeriya ne bisa bambancin yanki, addini ko kabila.
Manyan ‘yan siyasar sun cigaba da cewa bin tsarin ya sabawa damar mutane ta tsayawa takara ko da sun cancanta; kuma hakan zai kara hana wadanda ke da karbuwa ko hikimar jagoranci samun madafun iko.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.