Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da sauran manyan ‘yan siyasar Najeriya sun mika sakon ta’aziyya ga rasuwar tsohuwar ministar mata Aisha Jummai Alhassan da a ke yi wa lakabi da Mama Taraba.
Rahoto ya baiyana cewa marigayiyar ta rasu ne a kasar Masar.
Aisha Alhassan wacce ta tsaya takarar gwamnan jihar Taraba ta taba zama ‘yan majalisar dattawa bayan aikin da ta yi a matsayin magatakardar babbar kotun birnin taraiya Abuja.
Akalla dai za a ce ta na daga mata da su ka yi fice a lamuran siyasa a yankin arewacin Najeriya.
Ta samu sabani da fadar gwamnatin Najeriya gabanin zaben 2019 bayan mara baya ga tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar; inda hakan ya sa ta rasa tikitin takarar gwamna a inuwar APC karkashin shugaban Adams Oshiomhole da hakan ya ba wa Sanata Sani Danladi damar samun tikitin.
Your style is unique in comparison to other people I have read stuff from.
Thanks for posting when you have the opportunity, Guess I will
just bookmark this site.
Thanks for finally writing about > MANYAN 'YAN SIYASA NA AIKA SAKONNIN TA'AZIYYA GA RASUWAR MAMA
TARABA AISHA ALHASSAN – Noblen tv < Liked it!
I visit daily some websites and sites to read content,
except this blog provides quality based writing.