• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MANYAN MALAMAN AFGHANISTAN DA PAKISTAN SUN YI TARON KARFAFA SALAMA A MAKKAH

Manyan malaman Islama na kasar Afghanistan da Pakistan sun yi taro na musamman a birnin Makkah inda su ka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta hanyar sulhunta bangarori da ke yaki da juna.

Ministan aikin hajji da shiryarwa na Afghanistan Sheikh Muhammad Qasim Hamid da ministan lamuran Islama na Pakistan Sheikh Dr.Noor Al-Haq Qadri sun halarci taron.

Shugaban kungiyar kasashe musulmi De.Muhammad bin Abdulkarim Al-Issa ne ya jagoranci zaman da shi ne irin sa na farko da manyan malaman kasashen biyu makwabtan juna su ka zauna a teburi guda kan wannan batu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
39 thoughts on “MANYAN MALAMAN AFGHANISTAN DA PAKISTAN SUN YI TARON KARFAFA SALAMA A MAKKAH”

Leave a Reply

Your email address will not be published.