• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MANYAN HAFSOSHIN NAJERIYA SUN GANA DA SHUGABA BUHARI

Manyan hafsoshin tsaron Najeriya sun gana da shugaba Buhari a fadar Aso Rock inda su ka yi wa shugaban bayani kan halin da tsaro ke ciki.

Shugaban wanda ya yabawa hafsoshin amma lokaci guda ya bukaci su kara himma don inganta tsaron da ya tabarbare.

Da ya ke karin bayani bayan ganawar, babban sufeton ‘yan sanda Usman Baba Alkali ya ce shugaban ya yaba mu su amma ya bukaci su kara azama don magance kalubalen tsaron ta yanda dukkan al’ummar kasa za su sama salama.

Ba sabon labari ba ne yanda rashin tsaro ya zama ruwan dare a kusan dukkan sassan Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI馃榾馃榾馃榾
One thought on “MANYAN HAFSOSHIN NAJERIYA SUN GANA DA SHUGABA BUHARI”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *