• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MANJO NA SOJA DA A KA SACE A NDA KADUNA YA SAMU KAN SA

ByHassan Goma

Sep 18, 2021 ,

Manjo CL Datong da masu satar mutane su ka yi awun gaba da shi a lokacin da su ka kutsa makarantar horar da hafsoshin soja NDA da ke Kaduna, ya samu kan sa.

Kakakin rundunar soja ta daya ta Najeriya Kanar Ezindu Idimah ya ce an ceto Datong ta hanyar bata-kashi da barayin.

Idimah ya kara da cewa soja sun rugurguza maboyar barayin a yankin Afaka da ke jihar ta Kaduna.

Idimah ya kara da cewa bisa umurnin babban hafsan sojan kasa da kuma hadin guiwar jami’an DSS, sun bazama zuwa tungar barayin inda a ke rike da Dantong su ka yi musayar wuta har su ka ci karfin barayin su ka kwato sojan.

Duk da haka dai Manjo Dantong ya samu rauni amma an yi ma sa magani da mika shi ga makarantar ta NDA.

In za a tuna a lokacin harin, barayin sun yi kisan gilla ga jami’an soja biyu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *