• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MANJO JANAR FAROUK YAHAYA YA ZAMA BABBAN HAFSAN SOJAN KASA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nada Manjo Janar Farouk Yahaya ya zama sabon babban hafsan sojan kasa.

Nadin ya zo ne kimanin mako daya da rasuwar tsohon babban hafsan Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da tawagar sa a hatsarin jirgin sama a Kaduna.

Kafin wannan nadi, Manjo Janar Farouk na rike da kujerar babban kwamandan rundunar yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram a arewa maso gabar.

Wannan ya kawo karshen yayata sunayen wasu da a ke ganinza su samu mukamin ciki har da masu son a tura mukamin zuwa kudancin Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *