• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MANJO JANAR ABDUL KHALIFAH YA ZAMA KWAMANDAN RUNDUNAR HADIN GWIWA TA TAFKIN CHADI

Hafsan sojan Najeriya Manjo Janar Abdul Khalifah Ibrahim ya zama babban kwamandan rundunar hadin gwiwar yaki da ‘yan ta’adda na kasashen yankin tafkin Chadi.

Manjo Janar Ibrahim ya amshi ragamar daga tsohon kwamandan rundunar Jeleel Ongunalade a helkwatar ta da ke birnin Ndajamena na Chadi.

Tsohon kwamanda Ogunlade wanda shi ma dan Najeriya ne ya bukaci kulawa da dakarun da ke yaki a daji.

Ogunlade ya godewa sauran kungiyoyi kamar ta taraiyar turai da ke taimkawa wajen aikin rundunar da ke aikin yaki da ‘yan Boko Haram.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *