• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MANIYYATA AIKIN HAJJIN BANA SUN TSALLAKE RIJIYA DA BAYA DAGA KARAMAR HUKUMAR ISA A SOKOTO

ByNoblen

Jun 22, 2022

Maniyyata aikin hajjin bana daga karamar hukumar Isa a jihar Sokoto sun tsallake rijiya da baya a yayin da su ke tahowa Sokoto don tashi zuwa Saudiyya.

‘Yan bindiga sun kai hari kan kwambar motocin da ke jigilar maniyyatan amma Allah ya kubutar da su daga miyagun irin.

Rahotanni sun baiyana cewa ‘yan bindigar na fakewa ne a wani kungurmin daji inda su kan samu damar kai farmaki kan jama’a da samun kariyar duhuwar da su ke buya a ciki.

Tuni maniyyatan sun iso Sokoto inda za su keta hazo zuwa kasa mai tsarki.

Karamar hukumar Isa da Sabon Birni na daga yankunan da su ka fi samun illar hare-hare daga ‘yan bindigar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.