• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAN FETUR NA KARA ZAMA ABU MAI WUYAR SAMUWA A ABUJA

ByNoblen

Jul 6, 2022

Har yanzu ba a samu saukin neman man fetur a Abuja ba, don ya zama sai wasu gidajen mai kalilan ne kan iya sayar da man a kullum.

Lamarin ya kai ga samun dogayen layukan da kan kawo cikas ma a kan wasu tituna har ma ta kan kai ga hana masu wucewa bin layin hannun su.

Kazalika a kan samu mutane da kan kwana kan layin neman mai don dai su samu man cikin rahusa da kuma inganci.

Masu jarakuna na nan gefen gidajen mai su na sayarwa da dan karen tsada.

Hatta a daura da kamfanin main a NNPP masu jarakunan na nan su na tallar man su, kuma ala tilas mutane kan saya don in ba haka ba, motocin kan iya tsayawa cak.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.