• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAMMAN DAURA MUTUMIN KIRKI NE DA BA A FAHIMCE SHI BA – INJI SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammmadu Buhari ya ce dan uwan sa Mamman Daura mutumin kirki ne da jama’a ba su fahimta ba.

Shugaban wanda ke taya Mamman Daura murnar cika shekaru 81 a duniya, ya ce Daura na da dabi’un kwarai da gogewa kan lamuran mulki da na gwamnati da mutanen da su ka yi dacen hulda da shi kan amfana.

Duk da Mamman Daura ba shi da mukami na kai tsaye a gwamnatin Buhari, mutane kan gan shi kamar ‘yan-biyun shugaba Buhari ne don har tufar sawa iri daya su ke sakawa, kazalika a kan dauke shi babban jigo a tsara manufofin gwamnatin da alkiblar gwamnatin.

Duk da haka a kan samu sabani tsakanin bangaren Mamman Daura da Uwargidan shugaban Aisha inda har a ka taba kai ruwa rana tsakanin ‘yar Mamman Daura da Aisha a fadar ta Aso Rock.

Wannan dai sanarwar taya murna ce ta wajen mai taimakawa shugaban kan labaru Garba Shehu na nuna shugaban na matukar kaunar Mamman Daura kuma ya na bukatar sa cikin lamuran gwamnatin sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “MAMMAN DAURA MUTUMIN KIRKI NE DA BA A FAHIMCE SHI BA – INJI SHUGABA BUHARI”
 1. Heya! I understand this is sort of off-topic however I had to ask.

  Does building a well-established website such as yours require a
  large amount of work? I’m brand new to running a blog however I do write in my journal daily.
  I’d like to start a blog so I can share my experience and feelings
  online. Please let me know if you have any kind of recommendations or tips for brand new aspiring blog
  owners. Appreciate it!

 2. Wow that was strange. I just wrote an incredibly long comment but after I clicked submit my comment didn’t show up.
  Grrrr… well I’m not writing all that over again. Regardless,
  just wanted to say fantastic blog!

Leave a Reply

Your email address will not be published.