• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MALAMAI SU DAINA TSINE MA NA-MAI SATAR MUTANE BALERI

Madugun mai satar mutane a yankin Kaduna Sani Jalingo da a ke yi wa lakabi da BALERI ya bukaci malamai su daina tsine mu su don in su ka kara lalacewa kalubalen zai ta’azzara.

Baleri wanda shi ke rike da daliban jami’ar Greenfield na Kaduna ya ce ba zabin su ba ne zaman daji.

A zantawa ta wayar tarho, Baleri ya ce abun da su ke ji wasu malamai na fada a kan su ba sa jin dadi don wataran su na sa ran tuba.

Hakanan ga fatawar wasu malamai na nuna haramcin biyan kudin fansa; Baleri ya ce mutane su yi addu’ar kar su fada tarkon su.

Baleri ya ce ko gwamnan Kaduna Nasiru Elrufai ya shigo hannun su ba zai cigaba da matsayar ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.