• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAKIYAYA NA ARCEWA DAGA JIHAR ENUGU DON GUDUN CIN KARO DA ‘YAN BANGA

ByNoblen

May 31, 2021 , , ,

A yanzu haka makiyaya da dama na arcewa daga jihar Enugu don tsira da rayuwar su da dabbobin su.

Makiyayan da a ka zanta da su, sun ce tamkar farutar su a ke yi a jihar da sassan kudu maso gabar inda tuni a ka kashe wasun su da shanu da dama.

Daya daga makiyayan da kan yi kiwo tsakanin Enugu da jihar Kogi mai suna Yusuf Bature ya ce wasu jsmi’an banga kan kama makiyayan ko ma yin sanadiyyar ajalin su da dabbobin su matukar sun gamu da su a yankin jihar Enugu.

Bature ya bukaci gwamnatin taraiyar Najeriya ta kawo mu su dauki don tamkar yankin kudu ya zama ba ya bin dokokin hadin kan Najeriya.

Tuni jihohin kudu gaba daya su ka soke yin kiwo a fili a wani taro da su ka gudanar a garin Asaba na jihar Delta.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce matakin na gwamnonin kudu ya yi karantsaye ga tanadin tsarin mulki don haka ba za a amince da shi ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
46 thoughts on “MAKIYAYA NA ARCEWA DAGA JIHAR ENUGU DON GUDUN CIN KARO DA ‘YAN BANGA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.