• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAKAMAI MASU LINZAMI SUN YI DIRAR MIKIYA A TSAKIYAR KYIV

ByMardiya Musa Ahmed

Mar 16, 2022 ,

Makamai masu linzami na Rasha sun yi dirar mikiya a babban birnin Ukraine wato Kyiv a yayin da Rasha ta zafafa hare-hare don kammala yakin.
Sojojin Rasha na nausawa zuwa Kyiv inda makamai su ka bugi gine-ginen gidajen jama’a a birnin na Kyiv.
Daidai wannan lokaci shugabanni kasashen turai 3 za su nufi birnin Kyiv ta hanyar jirgin kasa don nuna mara baya ga Ukraine.
Shugabannin sun hada da na Czech, Slovenia da Poland.
Zuwa yanzu fiye da mutum miliyan uku ne su ka fice daga Ukraine don gujewa tsautsayin yakin.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce makaman sun fada kan gine-gine hudu a Kyiv inda gomman mutane su ka rasa ran su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
44 thoughts on “MAKAMAI MASU LINZAMI SUN YI DIRAR MIKIYA A TSAKIYAR KYIV”

Leave a Reply

Your email address will not be published.