• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR WAKILAI NA FUSHI DA MAI BA DA SHAWARA KAN TSARO NA NAJERIYA

Majalisar wakilan Najeriya na cikin fushi da mai ba da shawara kan tsaro na Najeriya Manjo Janar Babagana Monguno don yanda lamarin tsaro ya tabarbare.
A muhawarar ‘yan majalisar bisa jagorancin mataimakin kakakin majalisar Ahmed Idris, ‘yan majalisar sun nuna tamkar Monguno ya gaza don haka ya dace a sauya dabara.
Majalisar wacce ta duba irin harin da a ka kai kwanan nan kan jirgin kasa tsakanin Abuja da Kaduna da sauran lamuran tsaro, ta nemi ma a rufe majalisar don nuna juyayi da hakan ko zai taimaka a dauki matakan da su ka dace.
Muhawarar majalisar ta lura cewa yawancin barayin daji, yara ne kanana da bai dace a ce kwarewar su ta fi ta zaratan jami’an tsaron Najeriya ba.
Duk da haka an duba yanda a ka yi ta nuna damuwa da sai an sauya tsoffin manyan hafsoshin Najeriya don inganta tsaro, amma da alamu sauya su bai sauya lamuran ba.
Hakan dai tamkar kira ne ga gwamnatin taraiya ta farka don daukar matakan dawo da tsaro a birane da kauyuka ko ma a ce a dazuka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MAJALISAR WAKILAI NA FUSHI DA MAI BA DA SHAWARA KAN TSARO NA NAJERIYA”
  1. Hey there, You’ve performed a great job. I’ll definitely digg it and in my opinion recommend to my friends. I’m confident they will be benefited from this web site.

Leave a Reply

Your email address will not be published.