• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR SHUGABAN KASA TA YAMAN ZA TA MAIDA HANKALI GA ZAMAN LAFIYA

Majalisar shugaban kasa ta mulkin Yaman ta maida hankali wajen warware kuncin da al’ummar kasar ke fama da shi tsawon shekarun yakin basasa a kasar.
Tun kwace babban birnin kasar a 2014 da ‘yan tawayen houthi da Iran ke marawa baya su ka yi, a ke ta samun zubar da jini da asarsr dukiya da muhalli a kasar ta Larabawa.
Shugaban kwamitin jagorancin Rashad Al-Alimi ya nuna kwarin guiwar samun nasara bayan mika ma sa ragama da shugaba Abed Rabbo ya yi.
Kasashen duniya sun fi mara baya ga warware kalubalen Yaman ta tattaunawa a siyasance.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MAJALISAR SHUGABAN KASA TA YAMAN ZA TA MAIDA HANKALI GA ZAMAN LAFIYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.