• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR MINISTOCIN SAUDIYYA TA YI ZAMA A KARO NA FARKO A SHEKARU BIYU GABA DA GABA

A karo na farko a shekaru biyu, majalisar ministocin Saudiyya ta yi taro a waje daya kuma na gaba da gaba ba kamar yanda a kan yi a baya ta hanyar na’ura ba.
Sarki Salman ya jagoranci zaman a fadar Alyamamah da ke birnin Riyadh.
An karanto sako daga shugaban kasar Kudancin Sudan Salva Kir da ke bukatar hulda da Saudiyya, inda majalisar ta amince da yin hakan a duk wajen da ya dace.
Hakanan majalisar ta kawo batun hare-haren ‘yan tawayen houthi a Yaman, inda ta yi tir da yanda ‘yan houthi kan saba dokokin duniya a yakin basasar Yaman.
Mukaddashin ministan kafafen labaru Majed Al-qasabi ya ce majalisar ta nuna takaicin hare-haren houthi kan wajajen farar hula a Saudiyya da kuma Daular Larabawa.
Majalisar ta bukaci kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya dau matakan dakatar da miyagun laifukan houthi da su ka hada da barazana kan hada-hadar jiragen ruwa a tekun bahar maliya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.