• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR ISRA’ILA TA KWABE NETANYAHU DAGA FIRAMIMISTA

Majalisar dokokin Isra’ila ta kawar da Benjamin Netanyahu daga kujerar firaminista bayan mulkin tsawon shekaru 12.

Yanzu dai an rantsar da dan takarar gamaiyar jam’iyyu 8 Naftali Bennett ya zama sabon firaminista.

Netanyahu na cikin majalisar kasar KNESSET lokacin da ‘yan majalisa su ka kada kuri’a ta kankankan don mutum 60 kan 59 su ka amince da kafa sabuwar gwamnatin.

Netanyahu ya sha mamaki a majalisar don sai da ya tashi zai fice kafin ya juyo ya sha hannu da Bennett.

A na sa ran sabuwar gwamnatin da ke da hadin guiwar wata karamar jam’iyyar larabawa za ta bi hanyoyin da su ka dace wajen daidaitawa da Palasdinawa.

Kamar yanda mu ka ambata a wani labari, yawancin Palasdinawa na daukar kowanne shugaban Israila daya ne wato dabi’ar su ta muzgunawa Palasdinawa tamkar Danjuma ne da Danjummai.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *