• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR DOKOKIN ZAMFARA TA DAKATAR DA ‘YA’YAN TA 2 DON MURNAR SACE MAHAIFIN KAKAKIN MAJALISAR

 

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta dau matakin dakatar da ‘ya’yan ta biyu don zargin murnar da su ka nuna lokacin da barayin daji su ka sace mahaifin kakakin majalisar.

‘Yan majalisar biyu da a ka dakatar na tsawon wata uku sun hada da Ibrahim Tudu Tukur daga Bakura da Yusuf Anka daga Anka.

Mahaifin kakakin Alhaji Mu’azu Magarya ya riga mu gidan gaskiya a hannun barayin sanadiyyar bugun zuciya.

An ruwaito mai magana a madadin majalisar Mustapha Jafar na cewa ‘yan majalisar biyu za a baiyana gaban kwamitin dokoki don karbar ladabtarwa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MAJALISAR DOKOKIN ZAMFARA TA DAKATAR DA ‘YA’YAN TA 2 DON MURNAR SACE MAHAIFIN KAKAKIN MAJALISAR”

Leave a Reply

Your email address will not be published.