• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR DOKOKIN NAJERIYA TA TURA DOKAR TURA SAKAMAKON ZABE TA NA’URA GA SHUGABA BUHARI

ByYusuf Yau

Nov 20, 2021

Majalisar dokokin Najeriya ta tura dokar tura sakamakon zabe ta na’ura ga shugaban Najeriya Muhammadu don sanya hannu.
Dokar dai ta samu amincewar majalisar dattawa da ta wakilai don ba wa hukumar zabe hurumin amfani da na’ura wajen gudanar da zabuka.
Mai taimakawa shugaban Najeriya kan lamuran majalisa Babajide Omoworare ya baiyana tura dokar.
In dai shugaban ya sanya hannu, za a yi amfani da tsarin a zaben 2023.
A baya dai an samu ture kudurin gyaran dokar zabe gabanin zaben 2019 inda wasu su ka ce an yi gyaran ne don hana shugaba Bubari nasarar tazarce.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.