• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR DINKIN DUNIYA TA YI WATSI DA ZABEN SHAM

Majalisar dinkin duniya ta yi watsi da tsarin zaben da a ka gudanar a kasar Sham da bai ba wa ‘yan adawa damar takarar da ta dace ba kuma wasu ‘yan kasar ba su samu kada kuri’a ba.

Shugaban kasar Bashar Al’Asad ya kama hanyar cigaba da mulki na sabon wa’adin shekaru 7.

Jakadan majalisar dinkin duniya a Sham Geir Pederson ya ce zaben na daidai da murkushe tafarkin dimokradiyya kuma sam bai cika ka’idar zabe ta duniya ba, don haka ba zabe a ka gudanar ba.

Pederson ya yi kwamitin sulhu na majalisar jawabi kan zaben da nuna lalle keta duk wata doka ce da dama ga ‘yan adawar kasar.

Duk da haka kasar Rasha ce kadai a kwamitin ta ce sam ba a yi wa masu zabe a Sham adalci in an ce ba a gudanar da zabe ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.