• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR DINKIN DUNIYA TA YI TIR DA ZARTAR DA HUKUNCIN KISA KAN MUTUM 9 DA HOUTHI

ByHassan Goma

Sep 20, 2021 , ,

 

Majalisar dinkin duniya ta yi tir da yanda kungiyar ‘yan tawayen houthi a Yaman ta zartar da hukuncin kisa a bainal jama’a ga mutum 9.

Houthi ta ce ta samu mutanen da laifin kashe shugaban siyasar kungiyar Saleh Al-Samad shekaru 3 da su ka wuce don haka ta harbe su a bainal jama’a.

An ga wani jami’in lafiya na ba wa daya daga mutanen 9 ruwa a roba kafin harbe shi.

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya ce ba a bi tsarin dokokin duniya wajen kashe mutanen ba don ba a yi mu su hukuncin adalci ba.

Guterres ya bukaci dakatar da irin wannan hukunci da ya ce kidahumanci ne.

An jera mutanen 9 da tilasta su yin rub da ciki a kan dabe inda a ka harbe su ta baya.

Houthi ta ce mutanen 9 sun taimaka ta hanyar sanya katunan waya a aljifan jami’an tsaron Al-Samadi da hakan ya taimakawa rundunar Larabawa ta kai ma sa hari ta sama ta kashe shi yayin da ya ke ziyara a Hodeida don ingiza yin yaki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *