• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR DINKIN DUNIYA TA FARA TATTAUNAWA DON WARWARE TAKADDAMAR MULKIN SOJA A SUDAN

ByNoblen

Jan 11, 2022

Majalisar dinkin duniya ta dau matakin sa baki don magance fitinar da ta biyo bayan juyin mulki a Sudan da hakan ya jawo zanga-zanga da mutuwar fiye da mutum 50.
Gwamnatin sojan Sudan karkashin Janar Abdelfatah Burhan ba ta gwale majalisar kan matakin ba.
Wakilin majalisar kan Sudan Volker Perthes ya baiyanawa manema labaru cewa za a dau mataki na gaba don warware dambarwar.
Juyin mulkin ya jawo maida hannun agogo baya ga yanda turai ke son tallafawa Sudan bayan kawar da shugaba Omar Elbashir a 2019 da kasashen yamma ke adawa da shi.
Tsarin maida mulki ga farar hula a Sudan na nan a 2023 amma farar hula da ke adawa da soja na zargin sojojin za su share hanya ce don magoya bayan Elbashir ko shi kan sa Elbashir din kenan ya dawo kan madafun iko.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MAJALISAR DINKIN DUNIYA TA FARA TATTAUNAWA DON WARWARE TAKADDAMAR MULKIN SOJA A SUDAN”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *