• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR DINKIN DUNIYA TA BUKACI ISRAILA TA DAKATAR DA GINE-GINEN WUCE GONA DA IRI A FILAYEN PALASDINAWA

Majalisar dinkin duniya ta bukaci kasar Israila ta dakatar da kutsawa yankunan Palasdinawa da yin gine-gine don morewar Yahudawa.

Jakadan sakataren majalisar dinkin duniya a gabar ta tsakiya Tor Wennesland ya isar da bukatar ga sabuwar gwamnatin Israila karkashin firaminista Natfali Bennett.

Wennesland ya ce ya zama mai muhimmanci Israila ta yi amfani da kudurin majalisar dinkin duniya na 2016 da ya haramta aukawa yankunan Palasdinawa don gine-gine ga Yahudawa.

Israila na kutsawa gabashin burnin Kudus da yammacin gabar tekun Jodan ta na yin gine-ginen da hakan ya sabawa dokokin duniya.

Wennesland ya bukaci dakatar da kutsawar nan take.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MAJALISAR DINKIN DUNIYA TA BUKACI ISRAILA TA DAKATAR DA GINE-GINEN WUCE GONA DA IRI A FILAYEN PALASDINAWA”
  1. Definitely consider that that you stated. Your favourite justification seemed to be on the net the simplest factor to be mindful of.

    I say to you, I definitely get irked while people think about concerns that they just don’t realize about.
    You managed to hit the nail upon the top and also outlined
    out the entire thing with no need side effect , other people could take a signal.
    Will likely be again to get more. Thank you

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *