• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR DINKIN DUNIYA TA BUKACI DAKATAR DA HARI KAN MARIB

Ofishin ‘yancin ‘yan adam na majalisar dinkin duniya ya bukaci kungiyar ‘yan tawayen houthi da Iran ke marawa baya da makamai ta dakatar da kai miyagun hare-hare kan yankin Marib na Yaman.

Kwabakin baya ma houthi ta harba wani makami kan gidan mai a Marib inda fiye da fararen hula 20 su ka mutu ciki har da yarinya mai shekaru 5.

Kakakin ofishin Liz Throssel ta kawo misalai na hare-haren houthi kan farareb hula da hakan ya zama manyan laifukan yaki.

Jami’ar ta bukaci sassan biyu daga ciki  yakin su zauna kan teburin tattaunawa don dakatar da bude wuta na kasa baki daya.

Houthi na kokarin kwace Marib daga gwamnatin kasar don yankin na da arzikin iskar gas.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *