• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR DATTAWAN NAJERIYA BA TA BA DA KOFAR TATTAUNAWA KAN DAKATAR DA TWITTER BA

Majalisar dattawan Najeriya mai rinjayen ‘yan jam’iyyar gwamnati APC, ba ta ba da kofar muhawara kan dakatar da aiki da kafar sadarwar twitter da gwamnatin Najeriya ta yi bayan goge sakon shugaba Buhari kan masu kisan gilla da lalata dukiyoyin gwamnati a kudu maso gabar da kudu maso kudancin Najeriya.

Rashin samun damar a majalisar wakilai ya sanya ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP ficewa daga zauren majalisar don nuna fushin su.

Da alamu shugabancin majalisar na mutunta matsayar gwamnatin Najeriya ta rufe aiki da twitter don yanda kamfanin ke ba da damar ‘yan awaren IPOB na yada miyagun kalamai na tada tarzoma don kifar da gwamnatin farar hula ta Najeriya.

Duk da haka majalisar wakilan ta gaiyaci mimistan labaru Lai Muhammed ya baiyana gaban ta don karin haske kan dalilan gwamnatin na haramta aiki da twitter.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
41 thoughts on “MAJALISAR DATTAWAN NAJERIYA BA TA BA DA KOFAR TATTAUNAWA KAN DAKATAR DA TWITTER BA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.