• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR DATTAWAN AREWA TA CACCAKI GWAMNONIN KUDU DA IZA WUTAR RABA KASA

Majalisar dattawan arewa ta zargi gwamnonin kudancin Najeriya da iza wutar raba kasa ta hanyar matakai na kabilanci da aware.

Majalisar ta na magana ne kan matakin gwamnonin kudu na hana kiwo da daukar hakan a matsayin korar makiyaya daga kudu su dawo arewa.

Wannan na zuwa bayan shugaba Buhari ya amince da kudurin dawo da burtalin shanu da za a fara a watan gobe a jihohin da su ka ba da hadin kai don hakan ya kuma zama silar zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.

Hakanan matsayar ta dattawan arewa ba za ta rasa nasaba da matakin kafa rundunar tsaro ta Amotekun da kasashen yarbawa su ka yi don kare muradun su ba.

Akalla dai dattawan na arewa na ganin gwamnonin kudu na daukar matakai da ke barazana ga hadin kan Najeriya da marawa ‘yan awaren Biafra baya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.