• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR DATTAWA ZA TA DAUKAKA KARA KAN HUKUNCIN KOTU DA YA SOKE DOKAR ZABE TA 84

Majalisar dattawan Najeriya za ta daukaka kara kan hukuncin babbar kotun taraiya a Umuahia da ya soke dokar zabe mai lamba 84 da ta haramtawa masu rike da mukaman siyasa tsayawa zaben fidda gwani ko yin zabe a lokacin zaben na jam’iyyu.
‘Yan majalisar sun yi muhawara inda su ka nuna dokar ba ta saba da tanadin tsarin mulki ba, don tsarin mulkin ya na magana ne a kan ba da dama ga dan kasa ya tsaya takara amma ba batun shiga zaben fidda gwani ba.
Sanata George Sekibo ya nuna fargabar matukar ba a kalubalanci hukuncin ba, za a iya samun nan gaba a rika raina aiyukan majalisa ta hanyar duk wanda wata doka ba ta yi ma sa dadi ba sai ya garzaya kotu don soke dokar.
Ita ma majalisar wakilan ta dau irin wannan kudurin na kalubalantar hukuncin kotun a kotun daukaka kara.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MAJALISAR DATTAWA ZA TA DAUKAKA KARA KAN HUKUNCIN KOTU DA YA SOKE DOKAR ZABE TA 84”
  1. This is the right blog for anyone who wants to find out about this topic. You realize so much its almost hard to argue with you (not that I actually would want…HaHa). You definitely put a new spin on a topic thats been written about for years. Great stuff, just great!

Leave a Reply

Your email address will not be published.