• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR DATTAWA TA YI GYARA INDA TA BA DA DAMA GA ZABABBU SU IYA ZABE A TARON FIDDA GWANI

Majalisar dattawan Najeriya ta yi gyara a dokar zabe inda hakan zai ba da dama ga zababbu su samu damar kada kuri’a a lokacin zaben fidda da tarukan jam’iyya.
Wannan ya nuna majalisar ta yi gyara a sashe na 84 na sabuwar dokar zabe da kafin nan ta tsara sai wakilin da a ka zaba ne musamman zai iya yin zabe a fidda gwani.
Majalisar ta nuna wannan kuskure ne a ka samu da ba a yi niyyar ya faru ba kuma yanzu za a mika gyaran ga shugaba Buhari don sanya hannu.
Bayanin shi ne yanzu ‘yan majalisa da sauran zababbu za su iya kada kuri’a.
Gyaran da shugaba Buhari ya bukata a sashen na 84 na barin nadaddu a mukamai su iya tsayawa zabe ba tare da yin murabus ba, bay a cikin gyaran da majalisar ta yi.
Da alamu gyaran zai taimakawa ‘yan majalisar ne ya ba su damar gwagwarmaya da gwamnoni da sauran ‘yan sashen zartarwa a lamuran jam’iyya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
9 thoughts on “MAJALISAR DATTAWA TA YI GYARA INDA TA BA DA DAMA GA ZABABBU SU IYA ZABE A TARON FIDDA GWANI”
 1. I am not sure where you’re getting your information, but great
  topic. I must spend a while studying much more or working out more.
  Thanks for great information I used to be in search of this information for
  my mission.

 2. I’m not sure why but this web site is loading incredibly slow for me.
  Is anyone else having this issue or is it a issue on my end?
  I’ll check back later on and see if the problem still exists.

Leave a Reply

Your email address will not be published.