• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAJALISAR DATTAWA TA AMINCE DA BUKATAR KARBO BASHI NA SHUGABA BUHARI NA BILIYOYIN DALA

ByHassan Goma

Nov 11, 2021

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar karbo bashi da tuntuni shugaba Buhari ya mika da ya kai sama da dala biliyan 16.
Sauran aun hada da fam miliyan daya da kuma dala miliyan 125.
Wannan na cikin tsarin karbar lamuni ne na gwamnatin na shekara ta 2018-2020.
Majalisar ta amince da batun lamunin bayan karbar rahoto daga shugaban kwamitin kula da lamunin cikin gida da na ketare Sanata Clifford Ordia.
Majalisar dai ta dauki salon amincewa da lamunin daki-daki wato wannan karo ta amince da wannan bangare wani karon kuma ta sake amincewa da wani bangare.
Shugaba Buhari kan yabawa majalisar don yanda ta ke hulda da sashen zartarwa ba tare da samun cikas ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.